Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz ya bai wa alhazan – da ke kan hanyar koma wa ƙasashensu bayan kamma aikin Hajji – kyautar Al-Qur’anai.
Jaridar Saudi Gazzet ta ruwaito cewa a ranar Asabar ma’aikatar harkokin addinin musulunci da yaɗa da’awah ta ƙasar ta rabar da kofi 52,752 na Al-qur’ani mai girma ga alhazan da suka tashi a filin jirgin saman birnin Jedda.
Kyautar wata alama ce ta girmamawa da sarkin na Saudiyya ke yi wa alhazan da suka sauke farali.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya ce alhazan sun nuna jin dadinsu da yabo bisa kyautar karramawar da sarki Salman ya yi musu.
Kimanin mahajjata fiye da miliyan 1.8 daga ƙasashen duniya daban-daban ne suka sauke farali a wannan shekara.