Sarki Salman ya isa fadar Al-Safa da ke Makkah daga Jeddah a daren Juma’a domin kammala azumin watan Ramadan, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Saudiyya suka ruwaito
Hotunan da kamfanin dillacin labarai na Saudiyya SPA ya fitar a safiyar ranar Asabar sun nuna sarkin yana addu’a a Masallacin Harami.
Sarkin zai kammala watan Ramadan a Makkah tare da yin sallar idi a can.