Sarauniya Margrethe ta Denmark za ta yi murabus a yau Lahadi, bayan shekaru hamsin da biyu kan karagar mulki.
Za a nada babban ɗanta, Frederik, da matarsa Mary a matsayin sarki da sarauniya yau Lahadi.
Sarauniya Margrethe, wadda ta fi kowane basarake dadewa a kan karagar mulki a Turai, ta taba cewa ba za ta taba yin murabus ba, amma a wata sanarwa da ta yi ta ba-zata a lokacin bikin sabuwar shekara ta ce za ta sauka daga karagar mulki.
Sarauniyar mai shekaru tamanin da uku ta ce matsalolin lafiya sun sa ta sauya ra’ayinta.