Sarauniyar Elizabeth ta Ingila na biki cika shekaru casa’in da shida da haihuwa, a shekarunta na 70 kan karagar mulki.
Za ta shafe wunin yau a gidanta da ke Sandringham a Norfolk, sai dai za ayi harbin bindiga a fadarta da ke Landan da HydePark, sannan za su ayi kade-kaden gangar sojoji.
Sarauniya a watanni baya-bayanan tana ta fama da rashin isashen lafiya, ko da yake jikanta, Yarima Harry ya ce tana samun lafiya a wata hira da aka yi da shi a farkon makon nan.