fidelitybank

Sarau kiris a cimma yarjejeniya tsakanin Rasha da Ukraine

Date:

Ministan Harkokin Waje na Turkiyya Mevlut Cavusoglu da ke shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, ya ce an samu ci gaba tsakanin ɓangarorin biyu.

Cavusoglu ya faɗa wa kamfanin labarai na AFP cewa “ba abu ne mai sauƙi ba a cimma a matsaya yayin da ake ci gaba da fafata yaƙi, yayin da ake kashe fararen hula”, amma ya ƙara da cewa “mun ga alamun suna ƙoƙarin cimma yarjejeniya”.

Ministan ya ziyarci Rasha da Ukraine a makon nan sakamakon ƙawancen da Turkiyya ke yi da ƙasashen biyu. In ji BBC.

Ya ce Turkiyya na tuntuɓar tawagogin da ke tattaunawa da juna amma ya ƙi bayyana abin da tattaunawar ta ƙunsa saboda “Turkiyya na taka rawar mai sasanci ta gaskiya”.

Ɓangarorin biyu na yunƙurin cimma yarjejeniya a kan abu shida:

  • Ukraine ta zama ‘yar ba-ruwana
  • Ukraine za ta watsar da makamanta
  • Abin da Rasha ta kira “kakkaɓe ‘yan ta’adda daga Ukraine”
  • Cire duk wani tsari da zai hana amfani da harshen Rashanci a Ukraine
  • Matsayin yankuna biyu da suka ɓalle daga Ukraine na Donbass
  • Matsayin yankin Crimea da Rasha ta ƙwace a 2014

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya faɗa cikin wani bidiyo ranar Asabar cewa: “Wannan ne lokacin da ya kamata a haɗu, a tattauna, lokaci ne da za a fayyace iyakoki da kuma yi wa Ukraine adalci.” 

naija news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp