fidelitybank

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron Gwamnoni – Sarkin Musulmi

Date:

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Mohammad Abubakar II, ya musanta maganar da ake yi cewa sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnoni.

Sarkin musulmin ya ce sarakunan gargajiya sun kasance jagorori a ƙasar tun kafin ta samu ƴancin kai, sannan ya ƙara da cewa sarakunan sun fi gwamnonin fahimtar yanayin ƙasar.

Ya bayyana hakan ne a wani taro na ƙungiyar ci gaban matasan arewacin Najeriya da Gidauniyar Tunawa da Sardauna ta shirya a Abuja a ranar Talata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tun da farko, tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, ya bayyana cewa sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnoni.

Da yake mayar da martani, sarkin na Musulmi ya ce, “Na ji an ce sarakunan gargajiya na tsoron gwamnoninsu. Ba haka ba ne, sarakuna ba sa tsoron gwamnoni. Sarakunan gargajiya suna girmama kansu ne, sannan suna girmamma gwamnonin domin suna da iko a jihohinsu.

“Duk lokacin da wani abu ya faru, muna mayar da shi zuwa ga Allah ne. Muna kawo sauyi, kuma muna karɓar sauyi a yadda suka zo mana. Duk mun sani, akwai sarakunan gargajiya a Najeriya tun a shekarar 1824, amma a shekarar 1960 ce Najeriya ta samu ƴanci.”

punch news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp