Sarakunan biyu da ke hamayya da juna Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero sun bayyana shirinsu na yin sallar Juma’a a babban masallacin Juma’a na fadar.
Tuni Malam Muhammadu Sanusi II, wanda ke zaune a fadar, kuma kusa da Masallacin da ake fafatawa, ana sa ran zai jagoranci sallar Juma’a raka’a biyu.
Muhammadu Sanusi II ya jagoranci Sallar Juma’a a babban masallacin fadar a matsayin sarkin birnin, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Danburan Kano, Munir Sanusi Bayero, ta bayyana matsayar Maimartaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II zuwa Masallacin domin jagorantar Sallar Juma’a.
An fitar da sanarwar a daren Alhamis.
Sanarwar ta Danburan ta gayyaci mazauna Kano da su zo su saurari wa’azin da Malam Muhammadu Sanusi II zai gabatar.
Sai dai kuma wata sanarwa daga wani hadimin mai martaba Sarkin, Alhaji Aminu Ado Bayero ya gayyaci jama’ar yankin da su zo tare da shi a masallacin Juma’a na fadar Sarkin domin gudanar da sallar Juma’a.
An bayyana cewa za a fara tattakin zuwa Masallacin Sarkin da karfe 12:30.
Sai dai har yanzu ‘yan sandan ba su ce uffan ba kan wannan ci gaban. In ji Daily Post.