Jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya ta sauya sunan filin jiragen sama a jihar zuwa filin jiragen sama na Bola Tinubu, lamarin da ya janyo suka daga wasu ƴanƙasar.
Mai magana da yawun gwamnatin jihar, Hajiya Binta Mamman ta ce an sauya wa filin jiragen saman na ƙasa da ƙasa suna ne, domin gudunmawa ta fuskar ci-gaba da shugaban ƙasar ya baiwa jihar.
Sai da wasu al’ummar ƙasar sun yi suka ga matakin, suna ɗora ayar tambaya kan tasirin yin hakan ta fuskar tattalin arziki.
A ranar Litinin ne ake sa ran shugaba Tinubu zai kai wata ziyarar aiki jihar, inda zai ƙaddamar da filin jiragen saman da aka yi wa gyara da kuma wani wurin da aka ware domin ayyukan noma.
Kafin sauya wa filin jiragen saman suna, ana kiransa ne da filin jiragen saman Abubakar Imam, wani marubuci kuma ɗanjarida wanda ya fara ƙirƙiro jaridar harshen Hausa ta farko a arewacin ƙasar.
A shekarar da ta wuce ne hukumomin da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama suka ce za su sauyawa wasu filayen jiragen sama 15 na gwamnatin tarayya suna, zuwa sunayen wasu fitattun mutane, ciki har da tsaffin shugabannin ƙasar.