An zabi gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a matsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Yamma.
An dai zabi Sanwo-Olu a matsayin shugaba yayin taron su na shiyyar da suka yi a jihar Legas a yau.
Gwamnoni shida a yankin Kudu maso Yamma, sun dai zabi Sanwo-Olu baki dayan su.
Taron ya samu halartar gwamnoni da suka hada da Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo da Dapo Abiodun na jihar Ogun da Seyi Makinde na jihar Oyo da Ademola Adeleke na jihar Osun da kuma Biodun Oyebanji na jihar Ekiti.
Tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu wanda ya mutu watannin da suka gabata shi ne shugaban kungiyar na karshe kafin a samar da sabon shugaban kungiyar gwamnonin yankin Kudu maso Yamma.