Gwamna Babajide Sanwo-Olu a ranar Lahadin da ta gabata ya bayar da wa’adin kwanaki uku ga ‘yan kasuwa da ke karkashin gadar Apogbon da ke tsibirin Legas da su fice ko kuma a rushe wurin nan da ranar Laraba.
Sanwo-Olu ya yi wannan gargadin ne a lokacin da yake tuki a kan gadar, a lokacin da yake duba aikin layin dogo.
Ya ga ’yan kasuwar sun koma karkashin gadar tare da baje kolin kayayyakinsu bayan da aka kora su bayan barkewar gobarar, a karkashin gadar Apongbon kimanin makonni shida da suka gabata.
Gwamnan ya fusata kan komawar ‘yan kasuwar ba bisa ka’ida ba a karkashin gadar Apongbon, yana mai cewa za a tura tawagar jami’an tsaro zuwa gadar bayan wa’adin kwanaki uku.