Ƙungiyar sanatocin Arewa, ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu fararen hula 35 a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a jihar Zamfara.
Cikin wani saƙon jaje da ƙungiyar ta aike ranar Laraba a Abuja, shugaban ƙungiyar Sanata Abdulaziz Yar’adua,ya jajanta wa al’ummar yankin musamman iyalan waɗanda lamarin ya shafa.
A farkon makon nan ne ƴanbindiga suka yi wa su mutanen yankan rago duk kuwa da biyan kuɗin fansa da aka ce iyalansu sun yi domin kuɓutar da su.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da ayyukan ƴanbindiga masu sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Wasu masu sharhi dai na ci gaba da sukar gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar tsaron ƙasar kan rashin samar da zaman lafiya a yankin.