Rahotanni sun bayyana cewa Sanata Ayogu Eze daga jihar Enugu ya mutu.
Sanatan ya wakilci mazabar Enugu ta Arewa a majalisar wakilai ta kasa.
Wata majiya ta shaidawa DAILY POST cewa, Eze, tsohon kakakin majalisar dattawa ya rasu ne a wani asibitin Abuja bayan ya sha fama da jinya.
A cewar majiyar, marigayi Sanatan ya yi kasa a gwiwa, lamarin da ya sa ya kasa halartar bikin auren yaronsa da aka yi a farkon shekarar a jihar Legas.
Ya kasance dan jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, kafin ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC, inda ya tsaya takarar gwamnan jihar Enugu.