fidelitybank

Sanata ta maka Akpabio a kotu

Date:

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya ta shigar da shugaban majalisar ƙara a gaban kotu kan ɓata mata suna.

A ƙarar da ta shigar gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja ranar Talata, ‘yarmajalisar ta zargi Sanata Godswill Akpabio da mataimakinsa na musamman, Mfon Patrick, da yin kalaman ɓata suna a kanta.

Ta nemi kotun ta tilasta wa mutanen janye kalaman, su nemi afuwarta a wani shafin jarida, sannan su biya ta diyyar naira biliyan 100.

Ta ɗora zargin nata ne kan wani saƙo da ta ce Mista Patrick ya wallafa a shafinsa na dandalin Facebook, inda ya soke ta cewa “ba ta san komai ba game da zaman majalisa…da kuma saka tufafi masu shara-shara”.

A makon da ya gabata ne sanatar da shugaban suka yi cacar baki a zauren majalaisar bayan Akpabio ya sauya mata wurin zama, abin da ya jawo cecekuce tsakanin ‘yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta.

daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp