An ayyana Sanata Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na Edo.
Gwamna Bassey Otu na Kuros Riba wanda shi ne Shugaban zaben inuwar jam’iyyar APC na Edo, ya bayyana hakan bayan tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 18.
Okpebholo ya samu kuri’u 12,433 inda ya doke Dennis Idahosa wanda ya samu kuri’u 6,541.
An tattara tare da sanarwar a Lushville Hotel da Suites, Gapiona Avenue, Area Reservation Government (GRA), Benin.