fidelitybank

Sanata Mace ta farko a Najeriya ta rasu

Date:

Mace ta farko a Najeriya da ta fara zama Sanata, Gimbiya Franca Afegbua, ta rasu ta na da shekaru 81 a duniya.

Franca Afegbua wadda aka haifa a shekarar 1942, ta rasu ne da sanyin safiyar Lahadi a daya daga cikin asibitoci masu zaman kansu a birnin Benin.

Kassim Afegbua, daya daga cikin kannenta, dan jaridan da ya taba rike mukamin kwamishinan yada labarai a gwamnatin Adams Oshiomhole a jihar Edo, kuma a halin yanzu mamba ne a kungiyar yakin neman zaben Tinubu, ya tabbatar wa wakilin Daily Idependent.

Kassim ya ce ‘yar uwarta ta rasu ne da safiyar Lahadi kuma an kai gawar ta zuwa dakin ajiye gawa na UBTH.

Karanta Wannan: Tinubu zai gana da zababbun ‘yan majalisa

Sanata Gimbiya Franca Afegbua da aka zaba a kan turbar rusasshiyar jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN) a shekarar 1983, ta wakilci gundumar Bendel ta Arewa a tsohuwar jihar Bendel.

Ta yi aiki a babban zauren majalisar tarayya daga Oktoba zuwa Disamba 1983 kafin juyin mulkin soja na Buhari ya kawo karshen jamhuriya ta biyu a ranar 31 ga Disamba, 1983.

nigerian 
news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp