Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ‘yan sanda, Sanata Haliru Jika, ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar New Nigeria People’s Party a jihar Bauchi.
Jika, wanda a halin yanzu yake wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa, ya fito ne ba tare da hamayya ba, bayan ficewar Yusuf Ibrahim daga takara bisa radin kansa.
Shugaban zaben jam’iyyar NNPP Yusuf Kofar-Mata da Sakatarensa Mark Usman ya bayyana cewa hedkwatar jam’iyyar ta kasa ta aike su da su zo Bauchi su gudanar da zaben.
Delegates din dai sun amince da Jika a matsayin dan takara a cikin wata kuri’a.
Ya ce, “Bayan samun takardar janyewar Yusuf Ibrahim daga takarar, kuma da yake Sen. Haliru Jika a yanzu shi ne mai neman tsayawa takara, na tabbatar da shi a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a jihar Bauchi.
“Muna da wakilai 630 a nan tare da mu wadanda su ma suka tabbatar da Haliru Jika a matsayin dan takarar gwamna.
“Ina son in yaba wa jami’an hukumar zabe ta kasa (INEC) saboda kasancewarsu don ganin mun lura da duk abin da muka yi a nan a yau.


