Sanata Binos Dauda Yaroe na jam’iyyar PDP, ya sake lashe kujerar sanata da ke wakiltar kudancin jihar Adamawa a karo na biyu.
Da ake sanar da sakamakon zaɓen a ofishin tattara sakamakon zaɓen mazaɓar, INEC ta ce Binos ya samu ƙuri’u 146, 407, inda ya buge sauran ‘yan takara da ya fafata da su.
A cewar hukumar zaɓen, ɗan takarar APC Adamu Samaila Numan, shi ne ya zo na biyu da ƙuri’u 94, 828 yayin da ɗan takarar jam’iyyar Labour ya zo na uku da ƙuri’u 9, 444.