Samson Tijani yana fatan samun nasara a kungiyar Wolfsberger AC ta kasar Austria.
Kulob dinsa, Red Bull Salzburg da Wolfsberger sun amince da yarjejeniyar aro ranar Laraba.
Tsohon kyaftin din na Golden Eaglets yanzu zai shafe kakar wasa ta 2023/24 tare da Wolfsberger.
Tijjani dai bai buga kakar wasan data gabata ba saboda rauni, kuma a kwanan baya ya dawo atisaye.
Dan wasan mai shekaru 21 ya yi farin cikin haduwa da sabbin abokan wasansa.
“Na yi farin ciki da samun damar samun horo a Wolfsberger AC a kakar wasa mai zuwa kuma ina so in yi shekara mai kyau tare da kungiyar,” Tijani ya shaida wa shafin yanar gizon kulob din.


