fidelitybank

Samar da shugabanci na gari ne zai kawo wa Afrika cigaba – Tinubu

Date:

Shugaban Najeriya kuma shugaban ƙungiyar Ecowas, Bola Tinubu ya yi kira ga shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma da su fifita samar da shugabanci nagari ga mutanen yankin, saboda a cewarsa shi ne kawai hanyar inganta da ci gaban tattalin arzikin yankin.

Yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron ƙungiyar da aka gudanar a birnin Abuja na Najeriya, shugaba Tinubu ya ce tsarin shugabanci nagari ne zai magance tarin matsalolin da al’umomin ƙasashen yankin ke fama da su, kamar inganta rayuwa da samar da kyakkyawan yanayin samar da gaba mai ɗorewa.

Shugaban na Najeriya ya ce samar da shugabanci nagari ne zai iya magance matsalolin yunwa da talauci da rashin tsaro da rashin aikin yi da rashin daidaito da sauran matsalolin da suka yi wa yankin katutu.

”Ya kamata mu samu nasarar magance wasu matsalolin juyin mulkin soji a yankinmu”. in ji Tinubu.

Ya ci gaba da cewa lokaci ya yi da za a ƙarfafa tsarin dimokraɗiyya da mutuntu haƙƙoƙin talakawan yankin na zaɓar shugabannin da suke so.

“Yankinmu ya amince da ɗaukar tsaurara matakai ga duk wata ƙasa da ke cikin ƙungiyarmu da ta yi yunƙurin kawar da halastacciyar gwamnatin da talakawa suka zaɓa”, in ji Tinubu.

Yayin da takunkuman da za mu ɗauka ga ƙasa za su haifar da wasu matsalolin, yana da muhimmanci mu fahimci cewa muna koƙari ne wajen kare wa talakawa haƙƙoƙinsu tare da mutunta ‘yancinsu.

nigeria.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp