fidelitybank

Samar da matatun man fetur ba ya na nufin rage farashin man ba ne – NNPCL

Date:

Shugaban babban kamfanin mai na Najeriya NNPCL, Mele Kyari, ya ce ba rage farashin man fetur ba ne babban maƙasudin gina matatun mai a ƙasar ba, sai dai ya ce wataƙila hakan ka iya faruwa.

Mele Kyari ya faɗi hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin tsare-tsare da kasafin kuɗin majalisar dokokin ƙasar bisa gayyatar da majalisar ta yi masa.

Shugaban na NNPCL ya kuma ce ayyukan sabbin matatun za su inganta tare da haɓaka samar da man fetur a ƙasar cikin shekarar 2024, ta yadda ƙasar za ta zama babbar mai fitar da man fetur a shekara mai kamawa.

Ya kuma sake jaddawa cewa a yanzu kamfanin ne ke gudanar da harkokinsa ba tare da samun tallafin sisin kobo daga gwamnatin tarayya ba.

A ranar Laraba ne dai majalisar dattawan ta bai wa shugaban na NNPCL wa’adin sa’o’i 24 da ya bayyana a gabanta, yayin da a baya ya sha yin watsi da gayyatar da kwamitocin wucin-gadin majalisar ke yi masa, kan yadda kamfanin ya kashe naira tiriliyan 11 wajen gyara da kula da matatun man fetur na ƙasar tsakanin shekarar 2010 zuwa 2023.

A shekarar 2022 ne dai gwamnatin tarayya ta bai wa kamfanin cin gashin kansa, domin haɓaka tare da inganta harkokin man fetur a ƙasar.

A lokacin da yake gabatar da jawabi bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban ƙasar cikin watan Mayu, Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, lamarin da ya haifar da tashin farashin man a faɗin ƙasar.

Wani abu kuma da masana ke cewa ya janyo hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar, wadda ta fi kowacce yawan jama’a a nahiyar Afirka.

vgn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp