Akalla yara 3,000 ne wasu ‘yan bindiga suka kora daga makaranta a wasu kauyukan karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
Malam Sa’ad Salihu, Shugaban sansanin ‘yan gudun hijirar ne ya bayyana hakan a wata ziyara da manema labarai suka kai yankin ranar Litinin.
Salisu, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Cigaban Matasan Shimfida, ya ce, wasu daga cikin yaran suna makaranta lokacin da al’ummar yankin suka fara gudu daga yankin saboda ‘yan fashi.
Ya bayyana cewa, da yawa daga cikin ‘yan gudun hijirar, wadanda a halin yanzu suke makarantar sakandiren ‘yan mata ta gwamnati, Jibia, sun fito ne daga al’ummomin Kwari, Zango, Shimfida, Tsauni, Far Faru, Tsambe da Gurbin Magariya.
A cewarsa, babban koma baya ne a fannin ilimi, sakamakon yawan yaran da barayin suka kore su daga makaranta, inda ya ce, sama da ‘yan gudun hijira 15,000 ne a sansanin.
“Akalla mata da kananan yara 23 ne suka mutu a sansanin a cikin watanni hudu, ko dai sakamakon hauhawar jini ko damuwa, yayin da mata 35 suka haihu.
“Sama da yara 3,000 da ke sansanin a halin yanzu ba su iya samun ilimi a halin yanzu.”
“Daga al’ummar Shimfida kadai, muna da mutane 8,000 da ke wannan sansanin; Al’ummar Far Faru, sama da 7,000 da kusan 200 sun fito ne daga al’ummar Zango.
“Wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar na can a wasu sassan Jamhuriyar Nijar; baki daya, kimanin mutane 20,000 ne ‘yan fashin suka kori daga yankunansu.
“Amma ba dukkanmu muke kwana a nan ba saboda rashin katifu da ruwa da tabarmi da gidan sauro. Wasu daga cikin matan kan je gidajen ‘yan uwansu su kwana.” Salihu yace.
Salihu ya bayyana cewa, sun yi watsi da gonakinsu kuma ba su da wata hanya domin ‘yan bindiga sun kwace filayen.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta yi duk mai yiwuwa wajen farfado da tsaro a cikin al’ummarsu domin su dawo su ci gaba da rayuwarsu ta yau da kullum.