Yau ce ranar yaƙi da cutar ciwon hanta ta duniya, inda ake gangamin wayar da kai don kawar da cutar da kuma ƙarfafa gwiwar al’umma su rika yin gwaji don gano mutum yana dauke da cutar ko akasin haka.
Bincike ya nuna cewa cutar hanta nau’in Hepatitis B wadda aka fi samun ta a yankin Afrika, ta kasance mafi haɗari cikin nau’o’in cutar.
Miliyoyin mutane ne ke harbuwa da cutar duk shekara ba tare da sun sani ba, abin da ya sa ake ta kiraye-kiraye ga jama’a su riƙa yin gwaji a kai-a kai.
Likitoci sun bayyana cewa akwai cutukan hanta kusan kashi biyar da ake kamuwa da su walau ta hanyar shan gurɓataccen ruwa da abinci ko shan ƙwayoyi barkatai ko ta hanyar da aka bai wa mutum jinin da bai dace ba.
Likitoci na kallon cutar hanta a matsayin shu’uma saboda yadda take cin ƙarfin ɗan’adam kafin a gano ta. Wani ƙwararren likita a Najeriya,farfesa Musa Muhammad Borodo, ya ce cutar ta yi yawa a ƙasar, “Mutane biliyan biyu ke fama da cutar ciwon hanta, yayin da a Najeriya mutane sama da miliyan 20 ke fama da cutar”.
Ya ce “Alamomin cutar sun haɗa da, sauyin launin ido zuwa kalar rawaya, zazzaɓi, da amai, sai dai idan cutar ta yi ƙamari tana haifar da aman jini, da kunburun ciki da ƙafafu. Kuma idan aka yi rashin sa’a tana shafar ƙoda ko ta haddasa cutar kansa.”
Ciwon hanta na cikin manyan cutuka masu haɗari da ke addabar jama’a, abin da ya sa Hukumar Lafiya ta Duniya ta haɗa gangami don kawar da ita nan da shekara ta 2030, ta hanyar yi wa jama’a gwaji da kuma riga-kafi musamman ga ƙananan yara. In ji BBC.


