Ma’aikatar lafiyar Hamas da ke iko da Gaza ta ce mutum 9,061 ne aka kashe a Zirin Gaza, tun bayan fara wannan yaƙin ranar 7 ga watan Oktoba.
Wannan ya haɗar da ƙananan yara 3,760, kamar yadda ma’aikatar lafiuar ta ce.
Ta kuma ƙara da cewa fiye da mutum 32,000 ne suka jikkata sakamakon rikicin.