Majalisar Dinkin Duniya ta ce an tilastawa mutane dubu dari uku da arba’in a Gaza barin gidajensu yayin da Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta a yankin a matsayin martani ga harin da Hamas ta kai a ranar Asabar.
Ma’aikatar lafiya ta FalasÉ—inawa ta ce hare-haren bama-bamai a yanzu sun kashe sama da mutane dubu É—aya da dari biyu, da raunata sama da dubu biyar.
Da yake babu shiga ba fita, don haka babu damar kai kayan agaji.
FalaÉ—inawa dai suna kira da a samar da wata mashiga don kai kayan agaji da suka haÉ—a da kayan abinci da magunguna da man fetur.
Wani jami’in Masar ya ce kasar na kokarin tattaunawa da Isra’ila don ba da wannan dama.