fidelitybank

Sama da masu zanga-zanga 1,000 ake tsare da su a Najeriya – AMNESTY

Date:

Ƙungiyar kare haƙƙin dan adam ta Amnesty International, ta bayyana cewa sama da masu zanga-zangar tsadar rayuwa 1,000 ne ke tsare a hannun hukumomin Najeriya sakamakon shiga zanga-zangar ta baya bayan nan.

Zanga-zangar wadda aka gudanar tsakanin ranakun 1 zuwa 10 ga watan Agusta ta rikiɗe zuwa tarzoma a wasu sassan ƙasar, inda aka samu rahotannin sace-sace da lalata kadarorin gwamnati a wasu jihohi.

Hukumomin tsaro a Najeriyar sun ce sun kama mutane da dama da ake zargi da hannu a yamutsin.

To sai dai a cewar kungiyar ta Amnesty International, mutanen da aka kama yan ba ruwana ne.

Malam Isa Sanusi, daraktan kungiyar a Najeriya, ya ce a kama mutane mutum 632 a Jihar Kano, yayin da kuma a Sokoto an kama mutane za su kai 109 sannan kuma a Jihar Borno an kama mutum sama da 100.

“A Bauchi ma an kama mutane sannan kuma mun sami labarin cewa Kaduna ma an kama mutane za su kai 70, a Katsina ma mutum 70 aka kama.” in ji daraktan.

“To, mutanen dai suna rarrabe ne a duka jihohi, har yanzu ba mu gama ƙididdigewa ba amma zuwa yanzu ƙididdigar da muka samu kan mutanen da aka kama sun fi 100.” daraktan ta ƙara da cewa.

Daraktan ya kuma ce “a duk lokacin da aka yi irin wannan zanga-zangar, muna sane da cewa ana yin kame na kan mai uwa-dawabi sannan ana kama mutanen da suak yi laifi da waɗanda basu yi laifi ba inda a ƙarshe waɗanda zanga-zangar suka shiga ba tare da aikata laifin komai ba, sai a nemi wani laifi a laƙa masu wanda ba su aikata ba.”

“To kuma muna da bayanin cewa akasarin mutanen da aka kama, babu wani laifin da suka aikata, kawai zanga-zanagar suka shiga kuma aka kama su.”

nigeria 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp