Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta ce, ta yi nasarar jigilar maniyyata sama da 1,600 zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
Ayari na baya-bayan nan, wanda ya kunshi maniyyata 515, sun tashi ne a jiya Lahadi ta kamfanin jirgin Max Air.
Yunusa Muhammad, jami’in hulda da jama’a na hukumar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
Ya ce hakan ya kawo adadin maniyyatan da aka dauka daga jihar zuwa Saudiyya sun kai 1,612.
Ya ce a halin yanzu an fara tantance maniyyatan da aka shirya dauka a jirgi na hudu kuma a yau ne ake sa ran za su tashi.