Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta ce sama da ma’aikata miliyan 1.4 za a horar da su kan yadda za su yi amfani da tsarin rajistar masu kada kuri’a (BVAS) yadda ya kamata a babban zaben 2023.
Kwamishinan INEC na kasa, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a shirin gidan talabijin na Channels TV mai taken, “2022 In Retrospect, an Karshen Shekara ta Musamman.”
Bugu da kari, Hukumar ta ce tana da isassun BVAS don gudanar da zabe a rumfunan zabe 176,846 a fadin kasar.
Ya ce, “Muna so mu kara horar da ma’aikatanmu na wucin gadi ta yadda ba za mu samu mutanen da ba su san yadda ake amfani da BVAS ba da kuma dora ta kan fasaha da sauransu.
“Hukumar BVAS, wadda muka ce ita ce za ta kawo sauyi dangane da wannan zabe, tana nan. Kuma ina son tabbatar da cewa muna da isassun adadin BVAS da za a yi amfani da su wajen gudanar da zabe a rumfunan zabe 176,846 a fadin kasar nan.”