fidelitybank

Salihu Tanko Yakasai ya bar jam’iyyar APC

Date:

Tsohon mai taimaka wa a kafafen yada labarai, kuma Darakta Janar kan harkokin yada labarai da sadarwa na gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC.

Ganduje ya sauke Salihu Tanko Yakasai daga mukaminsa, bayan ya caccaki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
A wani taron manema labarai a ranar Litinin, Yakasai ya ce, ya daina zama dan jam’iyya mai mulki a ranar 21 ga Maris, 2022. In ji Daily Trust.

Ya ce, “Na kasance dan jam’iyyar APC a Najeriya tun kafuwarta, kusan shekaru goma da suka wuce, dai dai a watan Fabrairun 2013.”

“Abin takaici, da amanar da muka baiwa jam’iyyar APC (gwamnati da kuma jam’iyyar) sau biyu kenan (wa’adi na daya da na biyu) duk an ci amanar mutane, abubuwa sun zama mafi muni a cikin wa’adi na biyu. Fa’idar shakkun da muka baiwa jam’iyyar a zangon farko ya gushe yayin da muka kara zurfafa zuwa wa’adi na biyu, zan kuma sake tunani da tuntuba domin sanin makomata” in ji shi.

Ya kuma yabawa Ganduje bisa yadda ya bashi damar yi wa gwamnatinsa hidima sama da shekaru biyar

nnnnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ĉ´ansandan jihar Kaduna, sun buĈ™aci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi Ĉ™ungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban Ĉ™aramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp