Mohamed Salah ya tabbatar da cewa zai ci gaba da zama a Liverpool a kakar wasa mai zuwa, amma abokin wasansa Sadio Mane ba zai yanke shawarar makomarsa ba, sai bayan wasan karshe na gasar zakarun Turai na ranar Asabar.
Makomar Salah ta kasance babban batu yayin da ya shiga shekarar karshe ta yarjejeniyarsa a Anfield tare da tsawaita wa’adinsa.
An ba da shawarar cewa, dan wasan na Masar, wanda ke kan gaba a gasar cin kofin wajen zura kwallaye a Premier tare da Heung-Min Son da kwallaye 23 a kakar wasa ta bana, za a iya sayar da shi a bazara don gudun kar Reds ta rasa shi kyauta a shekara mai zuwa.
Amma da yake magana gabanin fafatawar da Real Madrid, Salah mai shekaru 29 ya bayyana karara cewa, ba shi da niyyar buga kwallonsa a wani wuri a 2022-23.
Da yake dakatar da bayyana shirinsa bayan karshen kakar wasa mai zuwa, ya ce: “Na mai da hankali ne kawai a kan kungiyar, kuma ba na son magana kan kwantiragi na. Amma zan ci gaba da zama a kakar wasa ta gaba, hakan ya tabbata.
“A raina, ba na mayar da hankali kan kwangilar a halin yanzu, ba na son son kai, na ce watanni biyu da suka wuce, komai ya shafi kungiyar yanzu.
Yayin da kwantiragin Mane kuma ya rage shekara guda ya ci gaba da zama, dan wasan ya yi hasashen zai ci gaba.