Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, a ranar Juma’a ya bayyana cewa, Mohamed Salah ba na siyarwa bane.
A jiya, an samu rahotannin cewa Al Ittihad ta shirya kashe fam miliyan 100 kan dan wasan mai shekaru 31.
Ita ma kasar Saudi Arabiya a shirye take ta maida Salah cikin ‘yan wasan da suka fi samun albashi a duniya.
Sai dai Klopp ya ce babu wata hanyar tuntubar dan wasan.
“Yana da wuya a yi magana game da labarun kafofin watsa labaru saboda babu wani abu da za a yi magana game da shi daga ra’ayinmu.
“Yana da mahimmanci a gare mu. Babu komai a wurin. Idan akwai wani abu amsar za ta zama a’a, “in ji Klopp.
Da aka tambaye shi ko ya amince cewa Salah ya jajirce a Liverpool, Klopp ya kara da cewa: “Kashi dari bisa dari.”


