Cincirindon mutanen da suka taru yayin da duhun almuru ya fara sauka a shingen bincike na Beitunia, inda dangi da magoya baya suka tsaitsaya suna jiran isar fursunoni.
Wata ‘yar karamar nasara ce, kamar yadda wasu suka bayyana.
“Alama ce ta kyakkyawan fata ga Falasdinawa da kuma ‘yan Isra’ila,” a cewar Mohammed Khatib, “cewa tsagaita wutar za ta ci gaba kuma za a dakatar da kashe-kashe”.
“Za mu so faruwar wannan al’amari ba tare da a ce Hamas ta kwashi mutanen da ta yi garkuwa da su ba,” ya shaida wa BBC, “amma ba don su ba, Isra’ila ba za ta bar wadannan mutanen su fito ba.”