Kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN ta yabawa gwamnatin tarayya, bisa cika alkawarin da ta yi a baya na ceto sauran mutane 23 da aka sace daga jirgin Abuja zuwa Kaduna.
Kwamitin da shugaban kasa ya kafa da babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya kafa domin duba yadda aka yi garkuwa da wadanda harin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya rutsa da su, ya tabbatar da sako sauran 23 da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su.
Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa, shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa sakin mutanen.
Ya ce ci gaban da aka samu ba wai kawai ya nuna cewa, hukumomi na son yin kasuwanci sosai ba, a’a, a shirye suke su samar da manufofin siyasa da ake bukata domin kawo karshen ta’addanci a sassan kasar nan.
“Muna yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa wannan ci gaba wanda ke nuni da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na yaki da makiyanmu a matsayin rashin tsaro,” in ji Okoh.