Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony J. Blinken, ya tattauna da zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Tinubu.
Blinken ya kira Tinubu ne ta wayar tarho a safiyar Laraban nan, inda ya nuna zimmarsa na ganin Amurka ta ƙara karfafa hulɗar dangataka da Najeriya, musamman ma da gwamnati mai zuwa.
Ya ce ƙasashen biyu sun ɗauki tsawon lokaci suna hulɗa mai kyau, inda ya ce yana so yaga ɗorewar hakan karkashin mulkin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Tinubu.
Tinubu da Blinken sun kuma tattauna kan muhimmancin gudanar da gwamnatin da za tafi da duka ƴan Najeriya da kara inaganta tsaro da kuma kawo tsare-tsare da za su taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasar.