Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na ganawa da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, bayan ya isa ƙasar a wata ziyara da ya kai ƙasashen Isra’ila da Jordan.
Wannan ce ziyara karo na biyu tun bayan ɓarkewar yaki tsakanin Hamas da Isra’ila.
Zai tattauna da jami’an Isra’ila kan yadda za a dakatar da hare-haren soji da fafatawa ta ƙasa.
Ya kuma ce zai ci gaba da matsa lambar ganin an ci gaba da shigar da agaji zuwa Gaza da kuma kwashe Amurkawan da suka maƙale a can.
A gobe Asabar ake sa ran, ministan harkokin Jordan, Ayman Safadi, zai gana da Mista Blinken.
Inda za su tattauna kan halin da Falasdinawa ke ciki a Gaza, da buƙatar daukr matakin gaggawa na dakatar da yaƙin, da bai wa farar hula kariya, yayin da ita kuma Isra’ila ya zama wajibi ta mutunta yarjejeniyar ƙasa da ƙasa.