Sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Ibrahim Kashim, ya sauka daga muƙaminsa.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan jihar shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Muktar Gidado ya fitar ranar Juma’a da maraice.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan jihar Bala Mohammed ya amince da murabus ɗin sakataren gwamnatin nasa, tare da gode masa bisa aikin da ya yi da gwamnatinsa. In ji BBC.
“Gwamna ya umarci shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jiha, Dakta. Aminu Gamawa, ya riƙe muƙamin a matsayin riƙo”, in ji sanarwar.