fidelitybank

Sakarci da Talauci ne ya sa aka shiga gida na yin sata – Matawalle

Date:

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya faɗa wa BBC Hausa cewa, sata aka je yi gidnsa, bayan gwamnatin jihar ta ce, ta ƙwato wasu motoci daga gidan nasa da gwamnan ya ƙi mayarwa gidan gwamnati.

A ranar Juma’a ne gwamnatin Zamfara ƙarƙashin jagorancin Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ta ce jami’an tsaro sun shiga gidajen Matawallae biyu, a Gusau da kuma Maradun, inda suka ƙwato motoci har 40.

Sai dai Matawalle ya ce “sakarci ne” da “talauci” ya sa aka shiga gidan nasa, yana mai cewa an sace kayayyaki ciki har da hijabin matansa.

“Dukkan ɗakunan matana babu wanda ba a shiga ba, har da hijabi na mata aka kwashe. Hatta irin murhun nan na garwashi, duka an saka cikin mota an tafi da su,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin motocin da aka kwashe ya saye su ne daga Amurka tun kafin ya zama gwamna saboda da ma sana’arsa ce sayar da motoci.

legit breaking news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp