fidelitybank

Sakamakon jarabawa zai fito a makon gobe – JAMB

Date:

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa JAMB, ta ce, sakamakon kashin farko na wadanda suka rubuta jarrabawar a ranakun Juma’a da Asabar za su fito ne a mako mai zuwa.

Shugaban JAMB, hulda da jama’a da kuma ladabi (PAP), Dakta Fabian Benjamin, wanda ya tabbatar wa jaridar The Nation a ranar Asabar.

Sai dai an tattaro cewa, hukumar za ta fara fitar da sakamakon ne daga ranar Litinin ko Talata.

Benjamin ya ce, duba sakamakon jarabawar UTME da na shiga kai tsaye zai bi irin tsarin da hukumar ta dauka a bara.

Wani jami’in hukumar ya yi watsi da batun sauya jadawalin jarabawar ga wasu ɗalibai da suka kasa yin jarrabawar UTME, sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a Legas da wasu manyan biranen kasar.

Jami’in hukumar ta JAMB ya ce, ya sabawa tsarin hukumar ta sake sanya jadawalin jarrabawar wasu a lokacin da wasu suka yi jarrabawar a gari daya ko kuma cibiya.

Jami’in ya kara da cewa, ɗaliban da suka fuskanci kalubalen na’ura ne kawai za su sake jarabawar, sakamakon cibiyoyinsu ne kawai za su samu damar sake jarabawar.

Majiyar ta ce: “Ba batun ruwan sama ba ne domin wasu sun rubuta. Haka Legas ta kasance. Ana ruwan sama, wasu sun zo rubuta jarrabawar.

“Tsarin da muke yi shi ne, muddin wasu sun rubuta wannan jarrabawar ba za mu iya sake sanya wa kowane dan ɗalibi lokaci ba.

jalingo news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp