fidelitybank

Sakamakon dukan likita Asibiti ya sanya suka hana gawa

Date:

Hukumomin asibitin koyarwa da ke Ilorin a jihar Kwara ta ƙi bayar da gawar wani mutum da ya mutu tare da kama ɗaya daga cikin ‘yan uwan mamacin bisa zargin lakaɗa wa wani likitan asibitin duka.

Jaridar Punch  ta ruwaito cewa, uku daga cikin ‘yan uwan mamacin mai suna Alhaji Saliu ne suka doki wani likita a sashen kula da masu buƙatar kulawar gaggawa na asibitin.

Saboda abin da suka kira ‘rashin kula’ da lilitocin suka nuna musu lamarin da a cewarsu ya sa ɗan uwan nasu ya mutu.

Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan rasuwar ɗan uwan nasu wanda ke fama da cutar sankarar jini.

Ɗaya daga cikin ‘yan uwan mamacin ya ce asibitin ya hana su gawar mamacin saboda faruwar lamarin.

Ya ƙara da cewa sun kai ɗan uwan nasu sashen kula da masu buƙatar kulawar gaggawa na asibitin wajen ƙarfe biyar na asubahin ranar Talata, kuma babu likitan da ya zo kan ɗan uwan nasu duk kuwa da irin roƙon da suka riƙa yi wa likitocin.

Shugabar ƙungiyar likitoci reshen asibitin Mrs Mrs. Elizabeth Ajiboye ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ”gamayyar ƙungiyar likitoci ta ƙasar ne suka umarci hukumomin asibitin da kada su bayar da gawar mamacin har sai an kama tare da gurfanar da mutanen da suka daki likitan a gaban kotu”.

Daga ƙarshe ta shawarci al’umma da su guji ɗabi’ar cin zarafin ma’aikatan lafiya.

leadership news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...

Farashin kayan abinci na rugu-rugu a Najeriya – NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin...

Kotun Kano ta ce a kamo mata Dagacin Tamburawa

Kotun Shari’ar Musulunci da ke shelkwatar Hisbah a Kano,...

Kotu ta ƙwace motocin gwamnatin Zamfara guda 40 daga hannun Matawalle

Kotun Daukaka Kara da ke a Sokoto ta tabbatar...

A na cigaba da gudanar da zaben cike gurbi harda Kano

Kano na ɗaya daga cikin jhihohin da ake kaɗa...

Mutane 12 sun mutu a wani hatsari a Kano – FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta...

Masarutar Rano ta haramta aurar da Yaran da ba su kammala karatun Firamare ba

Masarautar Rano a Kano ta haramta cire yarinya daga...

Matatar Dangote za ta fara jigilar mai kyauta ga gidajen mai

Matatar man Dangote za ta fara jigilar mai kyauta...
X whatsapp