fidelitybank

Sai yau muka samu umarnin kotu a kan tsige Sarki – Gwamnatin Kano

Date:

Yayin da ake cigaba da dambarwar saukewa da ɗora sabon sarki a jihar Kano, gwamnatin jihar ta ce, sai a ranar Litinin ta samu umarnin da ke hana ta rusa sababbin masarautu huɗu.

A ranar Juma’a da dare ne Aminu Ado Bayero ya koma Kanon bayan balaguron da ya yi a kudancin Najeriya, inda ya tarar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke shi daga gadon sarautar garin tare da mayar da Muhammadu Sanusi II kan karagar.

Gwamnan ya ɗauki matakin ne jim kaɗan bayan Majalisar Dokokin Kano ta rushe dokar masarautu da aka ƙirƙira a 2019, wadda ta ƙirƙiro sababbin masarautu huɗu.

Wannan ta sa Aminu Babba, mai muƙamnin sarkin dawaki babba a masarautar, ya kai ƙara wata kotun tarayya wadda ta ba da umarnin a dakatar da sauke Aminu Ado, da naɗin Sanusi a matsayin sarki, sannan a bar abubuwa a yadda suke har sai ta kammala sauraron ƙarar.

Sai dai kuma, gwamnatin Kanon ta bakin Kwamashinanan Shari’a Haruna Isa Dederi, ta ce sai bayan sun aiwatar da duk abubuwan da kotun ta hana sannan suka ga umarnin nata.

“Wannan umarni da ake ta yamaɗiɗi a kai sai a yau [Litnin]…da misalin ƙarfe 10:00 na safe sannan ma’aikacin kotun tarayya a nan Kano ya kawo min shi,” in ji shi.

“Tun da yau ce ranar aiki kuma sai yanzu muka karɓa, to sai a saurari abin da kotun za ta ce idan muka tura namu takardun [martanin].”

Wakilin BBC a Kano ya yi yunƙurin jin dalilin da ya jawo jinkiirin isar umarnin kotun daga ɓangaren waɗanda suka shigar da ƙara amma bai yi nasara ba.

Yanzu haka dai Muhammadu Sanusi II na zaman fada a babban gidan sarki na cikin gari, yayin da shi kuma Aminu Ado Bayero ke nasa zaman a gidan sarki da ke unguwar Nasarawa.

asuu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp