Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ya ce, duk da cewa akwai yiwuwar fafatawa tsakanin ƙasarsa da ƙasashen Yamma kai-tsaye, Rasha ba za ta so yin yaƙin nukiliya ba tsakaninta da Amurka ko ƙungiyar ƙawance ta Nato.
“Rasha ba ta taɓa niyyar aiki da makaman nukilya ba. Amma halin da ake ciki a Ukraine…ya nuna ƙarara cewa akwai yiwuwar gwabzawa da ƙasashen Yamma,” a cewar Ivan Nechayev kamar yadda kamfanin labarai na Interfax ya ruwaito.
A shirye Rasha take “ta ci gaba da bin tsarin cewa babu wanda zai yi nasara a yaƙin nukiliya, kuma bai kamata ma a harba su ba”, in ji shi.
“A matsayinta na wadda take da makaman nukiliya, Rasha za ta ci gaba da nuna dattako kamar yadda ta saba. Ba mu da niyyar yin rikici kai-tsaye da Amurka ko Nato.
“Kundin tsarin aikin soja na Rasha ya ba da damar harba nukiliya ne kawai idan aka kai mata hari da makaman ƙare-dangi, ko kuma idan aka yi mata barazana.” In ji shi a cewar BBC.


