fidelitybank

Sai Sojoji su fatattaki ƴanbindiga daga dazuka kafin a samu zaman lafiya – Ganduje

Date:

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce, dole sojoji su fatattaki ƴanbindiga su ƙwace dazukan Najeriya domin kawo ƙarshen rashin tsaro.

Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ta’aziyar jaje ga Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago bisa rasuwar gomman mutane a sanadiyar gobarar fashewar tanka a jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A wata sanarwa da sakataren watsa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, Edwin Olofu ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, Ganduje ya ce akwai buƙatar a ƙara ƙaimi, musamman wajen fatattakar ƴanbindiga daga dazukan Najeriya domin kawo ƙarshen yaƙin harkokin ƴanbindiga a ƙasar.

“Hanyar da za a magance wannan matsalar ita ce a ƙwace dazuka saboda ƴanbindigar nan a cikin dazuka suke zama. Me ya sa muka koma muna jira su kawo hari, kafin mu tare su? lokacin da nake gwamna, kira na yi ga gwamnatin tarayya da ta zuba sojoji a dajin Falgore, wanda hakan ya sa aka kafa sansanin horar da sojoji.

“Tun daga lokacin ne aka fatattaki ƴanbindiga daga dajin, kuma Kano ta samu zaman lafiya,” in ji Ganduje.

Da yake mayar da martani, Gwamna Bago ya yi godiya bisa ziyarar jajen, sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gyare titin Suleja-Minna domin rage yawaitar haɗura.

punch news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka ƴan Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aƙalla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...

Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya naɗa shi

Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta...

‘Yar Najeriya ta haihuwa a aikin Hajjin bana

Wata mata da ta je aikin hajji daga jihar...

Rashin nadi da jinkiri ne ya kawo rashin nasarar mu a kakar 2024/2025 – Kano Pillars

Kungiyar Kano Pillars ta yi imanin cewa jinkirin shirye-shiryen...
X whatsapp