Bulalliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya yi ikirarin cewa, ya shirya kalubalantar jagoran APC, Bola Tinubu, wajen cimma burinsa na zama shugaban ƙasa na gaba a Najeirya.
Sanatan ya yi wannan furucin ne ranar Jumu’a yayin da talabijin Channels cikin shirin Siyasa a Yau.
Sanata Kalu, ya ce, duk abin da Tinubu ke tunƙaho da shi a siyasan ce, to shi ma ya taka wannan mukamin, kuma ya na da mutane.
Sai dai ya ce, “Ba zan iya hana Tinubu takara ba, amma za mu haɗu filin zaɓen fidda gwani, inda za’a yi ta ƙare”. in ji Kalu.
Ɗan takarar shugaban ƙasa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya ce tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu, bai kai ya hana shi cimma burinsa na gaje kujerar Buhari ba.