Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, ya sake yin barazanar kulle bankuna, shaguna ko manyan kantunan da suka ki karban tsofaffin takardun kudi na N500 da N1000.
Abiodun ya ce zai yi hulda da duk wani dan kasuwa ko mai bada sabis da ya ki amincewa da tsofaffin takardun a matsayin takardar doka.
Domin cimma hakan, gwamnan ya ce mazauna jihar su kira shi a duk lokacin da wani banki ko babban kanti ya ki amincewa da tsofaffin takardun kudi, yana mai cewa zai rufe cibiyar kasuwanci.
Karanta Wannan: CBN ya umarci Bankuna su karbi tsofaffin kudi
A cikin wani faifan bidiyo da wakilinmu ya gani, Abiodun ya ce: “A yanzu haka ina mika takardar gargadi ga duk wata kasuwa, dan kasuwa, gidan mai, ma’aikacin banki da ke kin tsohuwar takardar naira; idan an sanar da ni, zan yi aiki da ku da cikakkiyar doka.
“ Kotun kolin Najeriya ita ce babbar kotun kasar. Kotun koli ta yanke hukuncin cewa tsofaffin takardun Naira sun ci gaba da zama a kan doka. An mayar da wa’adin zuwa ranar 31 ga Disamba.
“Zan kulle shagon ku idan sun ce mini ba ku karbi tsoffin takardun ba. Duk lokacin da ka ɗauki tsohuwar takardar zuwa bankuna kuma suka ƙi karɓa, kira ni. Zan kulle kofofin irin wadannan bankuna, ciki har da manyan kantuna.
“Kuna jigilar ƙungiyoyi da masu sufuri, kar ku ƙi tsohon kuɗin. Idan ka kai bankin aka ki, zan karba daga hannunka, in kai bankin da kaina,” Abiodun ya bayyana cikin karfi.