Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sha alwashin korar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu da wasu shugabannin jam’iyyar daga PDP.
Gwamna Wike ya yi wannan alkawarin ne a wajen kaddamar da aikin titi a karamar hukumar Ikwerre ta jihar Ribas a ranar Alhamis.
Wike ya dora laifin rashin nasarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa da aka kammala a kan wadanda ya ce sun ki bin kundin tsarin mulkin PDP. Ya yi alkawarin korar su daga jam’iyyar da fara aikin sake gina ta.
Gwamnan ya bayyana matakin a matsayin “kashi na biyu na yakin.”
A cewarsa: “Wadannan mutane sun bar jam’iyyar mu a 2014-2015, jam’iyyar mu ta sha kashi; sun sake dawowa, jam’iyyar mu ta sake yin rashin nasara.
Karanta Wannan: Asari ya bayyana irin gwamnan da zai gaji Wike
“Sun ruguza jam’iyyarmu. Za mu kore su daga jam’iyyar mu. Ba su da rawar da za su taka a jam’iyyarmu.”
Wike ya kuma caccaki shugabancin jam’iyyar PDP bisa zargin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta da rashin bin ka’idojin zabe a lokacin da su (PDP) suka ki bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Ya ci gaba da yin ba’a ga shugabannin jam’iyyar PDP da suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da INEC inda ya bayyana shugabannin jam’iyyar a matsayin “kungiyoyin dalibai”.