fidelitybank

Sai na baiwa gwamnonin PDP matsala a jihohin su – Wike

Date:

Ministan babban birnin Najeriya, Abuja, Nyesom Wike, ya sha alwashin haifar wa gwamnonin PDP matsaloli a jihohinsu idan ba su janye hannunsu daga rikicin siyasar jihar Rivers ba.

Wike ya bayyana haka ne ranar Asabar lokacin da yake jawabi a taron jam’iyyar PDP a jihar Rivers da aka gudanar a birnin Fatakwal.

Mista Wike dai na taƙun saƙa da gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara kan jagorancin jam’iyyar PDP a jihar.

A makon da ya gabata ne dai gwamnonin PDP suka fitar da sanarwa bayan taro, wadda shugabansu – gwamnan Bauchi, Bala Mohammed – ya karanta, inda ya ciki ya ce ƙungiyar gwamnonin PDP ta jaddada goyon bayanta ga gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara.

To sai dai a martanin da ya mayar, Ministan na Abuja ya zargi gwamnonin da yunƙurin ƙwace jam’iyyar daga hanunsa, abin da kuma ya ce ba zai saɓu ba.

“Ina son tabbatar muku cewa, ba wai ba za mu bari wani ya ƙwace PDP daga hannunmu ba ne, a a bari na gaya muku, na ji wasu gwamnoni na cewa za su ƙwace jam’iyyar su bai wa wani, to ina tausaya wa waɗannan gwamnoni, domin zan kunno musu wutar da ba za iya kashe ta ba a jihohinsu”, in ji shi.

“Idan Allah ya wanzar maka zaman lafiya a jiharka, kuma ka ce ba ka buƙatar zaman lafiyar, to duk abin da kake so za ka samu, domin kuwa masu iya magana na cewa kowa ya kwana lafiya shi ya so,” in ji Wike.

Tsohon gwamnan Rivers ya ce saboda gwamnonin na ganin wuyansu ya yi kauri, saboda wasu kuɗin da ya ce sun tara, shi yasa suke ƙoƙarin sa bakinsu a jiharsa, ”To ku shirya ni ma ina da jan wuyan da zan iya yi muku hakan a jihohinku”.

legit news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp