Shugaba Zelensky na Ukraine ya lashi takobin ƴantar da yankunan kasar da Vladimir Putin ke cewa sun zama wasu yankuna na Rasha.
A wani jawabi da ya gabatar cikin dare, ya bayyana cewa ya san yana tattare da kalubale, sai dai yana da kwarin-gwiwar nasara.
Sannan ya mayar da martani kan mamayar Rasha ta hanyar hanzarta shigar da kasar cikin kungiyar NATO- matakin da tabbas ya tunzura Moscow, duk da cewa babu tabbacin cewa za a bai wa kasar mamba a gaggauce.
Mista Zelensky ya zargi Rasha da shiga iyakarsu ta hanyar aikata kisa, yaudara da karerayi yana kuma mai cewa babu batun sulhu indai ba wai sabon shugaba aka yi a fadar Kremlin ba.