Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya gargaɗi Real Madrid cikin raha cewa ƙungiyar tasa na kan hanyar kamo ta a yawan kofunan Zakarun Turai na Champions League.
Real ta jinjina kofin na Champions League har sau 14, City kuwa sai a jiya Asabar ta ɗauki na farko a tarihinta.
“Muna kan hanyarmu,” kamar yadda ya faɗa cikin barkwanci bayan an tashi daga wasan.
“Idan suka yi barci, kamo su za mu yi.”
Man City ta ci kofin ne bayan doke Inter Milan 1-0 a birnin Istanbul na Turkiyya a gaban ‘yan kallo fiye da 74,000.