Fadar shugaban kasa ta kare matakin ta na jan ƙafa kan tura jirgin yaƙi samfurin Super Tucano, domin yakar barayin daji masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa a Arewa maso Gabashin kasar.
Fadar ta ce, kafin gwamnati ta sayi jiragen yaƙin daga Amurka, akwai yarjejeniyar da aka cimma gabanin cinikin, yadda Najeriya ba za ta faɗa kan laifukan take hakkin ɗan adam ba.
Mai magana da yawun shugaban kan harkar yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya sanar da haka a tashar talabijin ta Trust TV.
Garba Shehu na cewa: ”Ana bai wa sojoji horon soji ne, shugaban kasa ya san abin da ya ke yi. Fatan mu da zarar ya kammala aikin nan ya koma gida, kotun manyan laifuka ta duniya ba za ta gayyace shi saboda take hakkin dan adam ba. Don haka mu bar sojoji su yi komai bisa tsari, kuma tsari irin nasu a lokacin da ya dace.“
Mallam Garba ya kara da cewa: “Idan kana mu’amala da kasashe kamar Amurka, ya zama dole ka bibiyi ra’ayin jama’a da kare hakkinsu wannan ya na da matukar muhimmanci a gare su. A bayyane ta ke karara, sun sayar wa Najeriya jiragen yaki samfurin Super Tucano, amma ana bin tsarin da dokoki suka tanada wajen tabbatar da hakan.”
“Ka da ku manta tsohuwar gwamnatin Amurka ta Barack Obama ta ki sayar wa Najeriya jiragen yakin saboda zargin take hakkin dan adam, amma shugaba Buhari ya yi kokarin ganin an wanke wannan zargin. Don haka wannan ma za a yi amfani da su a lokacin da ya dace,’‘ in ji Garba Shehu.