Shugaban Jami’ar Abuja, Farfesa Abdul-Rasheed Na”Allah, ya ce dole ne dalibai masu neman gurbin karatu a jami’ar, su gudanar da gwajin shan ƙwaya a matsayin sharaɗi, kafin samun gurbin karatu.
Farfesan ya bayyana haka a wajen taron gabatar da jawabi kafin bikin yaye dalibai da suka kammala karatu karo na 27 a ranar Laraba.
Ya ƙara da cewa jami’ar na aiki da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA domin taimaka wa daliban da ke shan miyagun kwayoyi da nufin sauya musu hali.
A cewarsa, sanin matsayin mutum game da tu’ammali da kwaya, abu ne mai muhimmanci da nufin taimaka musu rabuwa da matsalar shaye-shaye.
Farfesa Abdul-Rasheed Na’Allah ya kuma bayyana cewa dalibai 7,128 ne za su kammala karatu a Jami’ar Abuja bana yayin bikin da za a gudanar ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba.