Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi Alla-wadai da kisan wasu ƴan jihar 12 a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato a hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗan’uwansu.
An ruwaito cewa mutanen su 31 sun taso ne daga garin Basawa da ke ƙaramar hukumar Zaria a jihar Kaduna cikin motar bas mallakin Jami’ar ABU Zaria, kafin su faɗa hannun maharan.
Nan take aka kashe 12 da kuma jikkata 11 lokacin da aka far musu.
Gwamna Uba Sani ya nuna kaɗuwarsa matuka kan lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta kama waɗanda suka aikata laifin da kuma hukunta su.
Ya sha alwashin cewa gwamnatin jihar ba za ta gajiya ba har sai ta ga an gurfanar da maharan.
“Lokaci ya yi da za mu kawo karshen irin waɗannan abubuwa na kashe mutanen da ba su yi laifin komai ba, musamman yayin tafiya tsakanin jihohi. Babu wata hujja ta far wa kowane ɗan Nijeriya a kowane ɓangare na ƙasar. Ya kamata mu dakatar da wannan ɗanyen aiki,” in ji gwamnan.
Ya kuma jajantawa iyalan waɗanda lamarin ya shafa, inda ya yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankali domin ana ƙoƙarin ganin an hukunta masu laifin.